Bangaren kur’ani, An fara gudanar da wani taron baje koli mai taken kur’ani da basira, wanda dakarun sama na jamhuriyar muslunci suka fara gudanarwa daga ranar farko ta wannan sabuwar shekara, tare da halartar wasu daga cikin manyan hafsoshi da kuma jami’ai gami da wakilan cibiyoyin addini na farar hula.
2011 Mar 26 , 17:49
Bangaren kur’ani, cibiyar kula da ayyukan kur’ani ta kasa ta sanar cewa, za a ware wani kasafin kudi na musamman a wannan shekara domin kara bunkasa harkokin koyarwa musulunci, musamman bisa sabon shirin da wannan cibiya take da shi, da ake sa ran aiwatar da shia acikin wannan sabuwar shekara.
2011 Mar 26 , 17:48
Bangaren kur’ani, an sayar da kwafin kur’ani mai tsarki guda dubu 400 wadanda aka tarjama, lamarin da ke tabbatar da cewa mutane masu bukatar sanin ilimin kur’ani mai tsarki suna karuwa a kowane lokaci a tsakanin al’ummar musulmi da suke rayuwa a wannan zamani.
2011 Mar 26 , 17:42
Bangaren kur’ani, an gabatar da shawara dangane shirin gudanar da gasar karatun kur’ani mai tsarki da za agudanar a garin Ahwaz na lardin Khozestan da ke gabacin jamhuriyar musulunci ta Iran, wanda ake sa ran gudanarwa a cikin wannan wata na farkon shekarar hijira shamsiyya.
2011 Mar 24 , 15:21
Bangaren kur’ani, an fitar da sakamakon gasar karatu da hardar kur’ani ta maikatan jami’ar azad da aka gudanar a reshenta dake lardin Khozestan tare da halartar malai da kuma wasu daga cikin jami’an gwamnatin lardin a cikin farkon watan nan.
2011 Mar 24 , 15:20
Banagren kur’ani, shugaban babbar cibiyar kula da ayyuakan kur’ani mai tsarki ta kasa ya bayyana cewa, sama mutane dubu hamsin ne suka yi rijistar shiga wani shiri na bayar da horo kan karatun kur’ani mai tsarki da za agudanar a cikin wannan shekara a sassa daban-daban na kasa.
2011 Mar 24 , 15:18
Bangaren kur’ani, an fara gudanar da wani baje koli na zane-zane kan kissoshin kur’ani, da kuma bayani kan abubuwan da za su faru a ranar tashin alkiyama, ranar da dukkanin bayi za su hadu da ubangijinsu domin fuskantar hisabi kan ayyukansu na rayuwar duniya.
2011 Mar 24 , 15:16
Bangaren kur'ani, Shugaban cibiyar cibiyar ayyukan kur'ani saminul aimma da ke garin Neka ya bayyana cewa wannan cibiya ta gudaar da wani zama na yin bita kan dukkanin ayyukanta da ta gudanar a cikin shekarar da ta gabata da kuwa wadanda za a yi a cikin wannan shekara.
2011 Mar 23 , 09:33
Bangaren kur’ani, An gudanar bukin kammala tilawar kur’ani mai tsarkida ake yi wa lakabi da nur, wadda a ka gudanar a karo na hudu a daren karshe na shekarar hijira shamsiyya, wanda cibiyar Imam Jawad (AS) kan dauki nauyin gudanarwa a garin Khomeini.
2011 Mar 22 , 15:33
Bangaren kur’ani, shugaban cibiyar kula da ayyukan kur’ani ta malayer ya bayyana cewa an bayar da takardun shedar kammala samun horon karatun kur’ani mai 180 ga dalibai da suka halarci wani shiri da cibiyar ta shirya gudanarwa, wanda ya samu nasara wajen samar da makaranta da suka halarci horon.
2011 Mar 22 , 15:32
Bangaren kur'ani, An bude wasu manyan cibiyoyin kula da harkokin kur'ani mai tsarki a sansanonin palastinawa 'yan gudun hijira da ke kasar Jordan, wanda cibiyar kula da ayyukan alkhairi ta kasashen musulmi ta bude.
2011 Mar 13 , 17:57
Bangaren kur’ani, an sanar da sunayen wadanda za su shiga gasar karatun kur’ani mai tsarki da za a gudanar a kasar Sri Lanka, wadda za ta hada da karatu wato tilawa da kuma harda gami da kiran salla, wadda jami’ar Al-mostafa ta kasa da kasa ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa.
2011 Mar 11 , 18:29