Bangaren kasa da kasa; dubban yan kasar Afganistan ne a ranar talatar da ta gabata sha shidda ga watan farvardin na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in suka ci gaba da gudanar da zanga-zangar yin Allah wadai da tofin Allah tsine da kona kur';ani da wani malamin coci ya yi a kasar Amerika a wani mataki na haddasa rikici da tashin hankali.
2011 Apr 07 , 14:23
Bangaren kasa da kasa; an fara rubuta sunayen masu son shiga gasar karatun kur'ani mai girma da harda ta sultan Hasan Albulakiya a kasar Burundi.
2011 Apr 04 , 15:26
Bangaren kasa da kasa;a ranar goma ga watan Urdebehesht na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in za a gudanar da taron girmama mahardata kur'ani a birnin Riyad fadar mulkin kasar Saudiya.
2011 Apr 04 , 15:25
Bangaren kasa da kasa: shugaban sashen da ke kula da bangaren harkokin kur'ani mai girma da kuma da harkokin addini a kasar Koweiti ya bada labarin fara gasar kasa da kasa ta harda da karatun kur'ani da tajwidi n kur'ani mai girma na babbar kyauta a Koweiti daga ranar ashirin da hudu ga watan Farvardin na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya.
2011 Apr 04 , 15:23
Bangaren kasa da kasa; a ranekun sha biyar zuwa sha bakwai ga watan farvardin na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya darektocin mu'asissoshin da jami'ansu na kasa da kasa za su fara ziyarar gain da ido a birnin Khartum fadar mulkin kasar ta Sudan.
2011 Apr 04 , 15:22
Bangaren kasa da kasa;al'ummar kasar Afganistan a ranar sha uku ga watan Farvardin na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da yin Allah kona kur'ani mai tsarki da wani kirista ya yi a kasar Amerika kuma sun gudanar da wannan zanga-zangar ce a birnin Kandahar na kasar Afganistan.
2011 Apr 04 , 15:21
Bangaren kur'ani, babban jami'i mai kula da mai kula da harkokin kur'ani mai tsarki na garin Aran ya bayyana cewa, cibiyar ta gabatar da wani tsari da ta shirya ga ma'aikatar ilimi, da ya shafin koyar da dalibai a makarantun share fagen shiga makarntun firamare na kasa baki daya.
2011 Apr 03 , 15:10
Bnagaren kur'ani, An gudanar da shirin kur'ani mai tsarki na ranakun hutun idin nouruz, wanda babbar cibiyar kula da harkokin kur'ani mai tsarki da shirya gasa ta dauki nauyin shiryawa da gudanarwa, da nufin kara karfafa mahardata da kuma makaranta na kasar.
2011 Apr 03 , 15:10
Bangaren kur'ani, babban jami'i mai kula da hulda da jama'a na rundunar sojin jamhuriyar muslunci ta Iran ya bayyana cewa, ana shirin gudanar da wani zaman taro da ya shafi debe kewa da kur'ani mai tsarki, da ya shafi jami'an soji na jamhuriyar muslunci, tare da halartar manyan hafsoshi.
2011 Apr 03 , 15:09
Bangaren kur'ani, kimanin mutane 100 ne suka samu halartar wani taro na bayar da horo kan addu'arr sahifa sajjadiyya, da nufin sanin yadda ake karantawa da kuma salon a musamman a kan yadda za ta bayar da ma'ana da natsuwa ga ruhi mutum mai imani.
2011 Apr 02 , 19:13
Bangaren kur'ani, za a gudanar da wata gasar karatun kur'ani mai tsarki da ta kebanci dakarun sama na jamhuriyar muslunci ta Iran, da za ta hada da matansu da kuma yaransu gami da su kansu, domin kara karfafa gwiwarsu kan harkokin kur'ani mai tsarki.
2011 Apr 02 , 11:28
Bangaren kur’ani, za a gudanar da gasar karatun kur’ani da harda da ta kebanci daliban jami’a a kasar Malazia, wadda za ta hada har da dalibai ‘yan kasashen ketare da sukae karatu a jami’oi daban-daban na kasar Malazia, da nufin karfafa harkokin kur’ani a tsakanin dalibai.
2011 Mar 28 , 15:07