IQNA

Masu ziyara miliyan 22 ne suka ziyarci Karbala a lokacin Arbaeen na bana

16:13 - September 06, 2023
Lambar Labari: 3489770
Karbala (IQNA) Maziyarta sama da miliyan 22 suka yi ziyara a Karbala a cikin kwanakin Arba'in, da bayyana nasarar shirin na musamman na Arbaeen da firaministan kasar Iraki ya yi da jigilar masu ziyara sama da dubu 250 zuwa kasar Iraki.
Masu ziyara miliyan 22 ne suka ziyarci Karbala a lokacin Arbaeen na bana

Kamfanin dillancin labaran Mowazin ya habarta cewa, haramin Sayyid Abul Fazl al-Abbas (AS) ya sanar da cewa sama da maziyarta miliyan 22 ne suka halarci taron Arbaeen na bana a birnin Karbala.

Cibiyar Hubbaren Abbasi ta bayyana a cikin wata sanarwa cewa: Adadin maziyarta Arbaeen na Imam Husaini (AS) a Karbala ya kai miliyan 22 da dubu goma sha tara da 146.

Muhammad Shiyaa al-Sudani, firaministan kasar Iraki ya bayyana nasarar gudanar da shirin ziyarar Arbaeen na Imam Husaini (AS) a wata ganawa da ya yi da kwamandojin tsaro da gwamnan Karbala.

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta kasar Iraki ta sanar a yau Laraba cewa, adadin jigilar maziyarta a zuwa kasar Iraki a lokacin Arbaeen ya kai jigilar jiragen sama fiye da 1,850, wadanda ke dauke da masu ziyara daga kasashen duniya.

Ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar Iraki ta sanar a yau Laraba cewa, shirin na musamman na tsaro na Arbaeen zai ci gaba da kasancewa har sai masu ziyara na karshe sun koma kasashensu.

Kakakin ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Iraki Khalid al-Mahna ya bayyana cewa: Tsare-tsare na musamman na tsaron Arba'in ya kasance cikin nasara tare da gamsuwar al'ummar kasar, kuma daya daga cikin dalilan da suka sa aka cimma nasarar wannan shiri shi ne gagarumin shirye-shirye da kuma kyakkyawan tsari.

 

 

4167354

 

captcha