IQNA

Wani yunƙuri na wata ƙaramar hukuma a Turkiye don ƙarfafa yara wajen yin sallah

14:46 - August 26, 2023
Lambar Labari: 3489708
Istanbul (IQNA) Karamar Hukumar Janik da ke Turkiyya ta karfafa wa yara zuwa masallaci da yin sallah ta hanyar aiwatar da wani sabon tsari.

Kamfanin dillancin labaran kur’ani na iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na tashar Aljazeera cewa, a cikin wannan shiri mai suna ‘’Ya’ya mu je masallaci, mu yi murna da wasa’’, karamar hukumar ta bayar da kyaututtuka da suka hada da kekuna ga yaran da suka halarci masallacin tare da gabatar da addu’o’i ga Allah Kwanaki 30.

Karamar Hukumar Janik ta bayyana ta hanyar buga hotunan bikin karramawar cewa an baiwa yara kekuna 1160.

Daruruwan yara tare da iyalansu ne suka halarci bikin raba kyautuka a dandalin Adnan Menderes da ke birnin Janik. Hotunan da aka buga na wannan bikin sun nuna matukar farin cikin da yaran suka samu na samun wadannan kyaututtuka.

Ita ma karamar hukumar Janik ta sanar da wallafa wani sako a shafinta na dandalin sada zumunta na X cewa: ‘ya’yanmu sun halarci masallatan yankin a wani bangare na wannan shiri, kuma sun kasance masu hazaka a salloli biyar na masallatan, kuma mun gabatar da su kyaututtuka don ƙarfafa waɗannan yara ..

A cewar Ebrahim Tomanchi, magajin garin Janik, ta hanyar wannan aikin, an yi ƙoƙari don ƙarfafa sauran dabi'un dabi'u kamar tsari, nauyi da kuma horo ga yara.

Birnin Janik yana arewacin Turkiyya, kusa da Samsun, sanannen tashar jiragen ruwa na Turkiyya a gabar tekun Black Sea.

ابتکار یک شهرداری در ترکیه برای تشویق کودکان به نماز خواندن + عکس

ابتکار یک شهرداری در ترکیه برای تشویق کودکان به نماز خواندن + عکس

4165001

 

Abubuwan Da Ya Shafa: yara kyautuka halarci dandali sallah
captcha