IQNA

Qatar Ta Ware Dala Miliyan 500 Domin Sake Gina Wuraren Da Isra’ila Ta Rusa A Gaza

23:42 - May 27, 2021
Lambar Labari: 3485954
Tehran (IQNA) gwamnatin kasar Qatar ta ware dalar Amurka miliyan 500 domin sake gina wuraren da Isra'ila ta rusa a yankin zirin Gaza.

Shafin yada labarai na Sahab ya bayar da rahoton cewa, Ministan harkokin wajen kasar Qatar Muhammad Bin Abdulrahman Al Thani ya sanar a yammacin jiya cewa, bisa umarnin sarkin Qatar, gwamnatin kasar ta ware dala miliyan 500 domin sake gina yankin zirin Gaza.

A cikin bayanin da ya rubuta a shafinsa na twitter, ministan harkokin wajen kasar ta Qatar ya bayyana cewa, kasarsa za ta ci gaba da kare hakkokin al’ummar falastinu, tare da bin dukkanin hanyoyi na diflomasiyya, domin ganin an yi adalci wajen bai wa Falastinawa damar kafa kasarsu mai cin gishin kanta kamar yadda yake a cikin kudirin majalisar dinkin duniya.

3973994

 

captcha