Tashar CNN ta bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da gwamnatin Masar ta fitar a yau an bayyana cewa, daga yau an rufe dukkanin wurare na ziyara ta addini a kasar domin kaucewa yaduwar cutar corona a tasakanin jama'ar kasar.
Dauka wannan mataki dai ya zo ne bayan tattaunawa tare da malaman adini, da uam samun umarni daga babban malamin cibiyar ahzar Sheikh Ahmad Tayyib, da kuma malaman darikun sufaye.
Sanarwar ta ce wannan mataki na takaitaccen lokaci ne, wanda zai kawo karshe da zaran an samu saukin yaduwar cutar corona wadda ta addabi duniya a halin yanzu.
A daya bangaren cibiyar Azhar ta sanar da dakatar da dukkanin sallolin jam'i a masallatan kasar, kamar yadda aka dakatar da taruka na addini baki daya.