IQNA

A Masar Za A Gudanar Da Sallar Idi A Babban Masallaci Daya Ne

22:50 - July 26, 2020
Lambar Labari: 3485024
Tehran (IQNA) mahukuntan masar sun sanar da cewa, a kasar za a gudanar da sallar idi a masallaci guda daya ne.

Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, Musatafa Madbuli fira ministan kasar Masar ya bayyana cewa, a babbar salla kamar karamar salla da ta gaba ne. za  ayi sallar idi a masallaci daya ne.

Ya ce bisa la'akari da halin da ake ciki na yaduwar cutar corona, dole nea  ci gaba da daukar matakan da suka dace domin dakile yaduwar cutar a tsakanin jama'a.

Kamar yadda ya jadda cewa hatta a inda za a gudanar da sallar, za a dauki matakan da suka dace na kiyaye kaidoji kiwon lafiya.

A halin yanzu dai a kasar Masar akwai mutane 91,583 da suka kamu, yayin da 4,558 suka rasa rayukansu.

 

3912756

 

Abubuwan Da Ya Shafa: masar cutar corona suka kamu mutane gudanar
captcha