Kamfanin dillancin labaran IQNA ya bayar da rahoton cewa, gwamnatin Japan ta sanar da cewa, wadannan kuadde suna daga cikin irin taimakon da ta saba yi na jin kan dan adam ga alummar falastinu.
Cibiyar taimaka ma falastinawa da ke karkashin majalisar dinkin duniya ta bayyana cewa, za a yi amfani da kudaden ne wajen gudanar da ayyuka na taimaka ma mata da kananan yara, kamar yadda kuma za a yi amfani da wani bangaren kudade wajen gudanar da wasu ayyka a bangaren kiwon lafiya tare da hadin gwiwa da red cross.