IQNA

Taro Mai Taken Tunanin Imam Khoeini A Kan Kur’ani A Senegal

22:35 - June 07, 2018
Lambar Labari: 3482734
Bangaren kasa da kasa, a yau ne za a gudanar da zaman taro mai taken tunanin Imam Khomeini (RA) a kan kur’ani mai tsarki a Senegal.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a daen yau ne za a gudanar da wani zaman taro mai taken tunanin Imam Khomeini (RA) a kan kur’ani mai tsarki a Senegal tare da halartar shugaban karaminin ofishin jakadancin Iran a kasar.

Wannan taro dai yana zuwa ne a daidai lokacin da aka gudanar da tarukan tunawa da cika shekaru ashirin da tara da rasuwar Imam a Iran da ma wasu kasashen duniya.

Marigayi Imam dai yana ganin kur’ani mai tsarki a matsayin tsarin rayuwa ga dukkanin musulmi, kuma yin aiki da koyarwasa shi ne mafita ga dukkanin matsalolin dan adam.

3720767

 

 

 

 

 

captcha