IQNA

An Raba Kwafin Kur’ani Tarjamar Iran A Baje Kolin Senegal

22:46 - March 06, 2018
Lambar Labari: 3482456
Bangaren kasa da kasa, an raba kwafin tarjamar Iran a wani baje kolin kayan tarihin musulunci a Senegal.

An Raba Kwafin Kur’ani Tarjamar Iran A Baje Kolin SenegalKamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na bangaren hulada da jama’a na cibiyar yada al’adun muslunci ya habarta cewa, a jiya an raba kwafin tarjamar Iran a wani baje kolin kayan tarihin musulunci a jami’ar Dakar.

Bayanin ya ce wannan baje kolin ya hada da allunan rubutun ayoyin kur’ani da aka rubuta da fasaha ta musamman, kamar yadda aka nuna wasu alluna da suke dauke wuraren tarihin musulunci.

Karamin ofishin jakadancin Iran a Senegal ya nuna wasu daga cikin hotunan muhimman wurare na tarihin musulunci da suke a cikin kasa Iran, kamar yadda aka raba kwafin kur’ani da aka tarjama a cikin harshen faransanci a kasar Iran a wannan baje.

3697571

 

 

توزیع قرآن مترجم ایرانی در نمایشگاه سنگال

توزیع قرآن مترجم ایرانی در نمایشگاه سنگال

 

 

captcha