IQNA

Musulmin Masar Suna Kare Majami’un Mabiya Addinin Kirista

16:56 - December 22, 2014
Lambar Labari: 2625019
Bangaren kasa da kasa, mabiya addinin muslunci a kasar Masar suna bayar da kariya ga majami’un mabiya addinin kasar daga hankoron ‘yan ta’adda masu tsatsauran ra’ayi da ke barazana ga wadannan wurare.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanr gizo na radiovaticana cewa, a lokuta da dama mabiya addinin muslunci a kasar Masar suna bayar da kariya ga majami’un mabiya addinin kirista kasar daga hankoron ‘yan ta’adda.
Sabon Jagoran mabiya darikar katolika Fafaroma ya yi kira ga Chochin  ya ci gaba da yunkurinsa na tattaunawar fahimtar juna da sauran addinai musamman addinin musulunci. Fafaroma ya kuma ce, yin tattaunawa da musulmi yana da muhimmanci sosai wajen wanzar da zaman lafiya.
Da yake jawabi ga jakadu a fadar Vatican, ya bukaci cocin ya yi wa'azantarwa ga wadanda basu bada gaskiya ba domin yakar abin da ya kira mutuwar zuci da koma bayan tarbiyya a wannan zamani ,Ya kuma yi kira da a sabunta yunkuri wajen yaki da talauci da kuma kare muhallia douk fadin fadin duniya.
Msulmin kasar Masar suna taka gagarumar rawa wajen samun hadin kai tsakanin mabiya addinai na kirista da kuma musulmi a kasar da ma duniya baki daya.
2624785

Abubuwan Da Ya Shafa: vatican
captcha