Bangaren kasa da kasa: a karon farko za a gudanar da gasar karatun kur'ani mai girma da makarantar musulunci ta Almahdi ta shirya a lardin Pansilvaniya na kasar Amerika.
2012 Feb 21 , 18:15
Bangaren kasa da kasa; kasar Chana ta guduri aniyar gina gurin ajiya da ganin kur'ani masu tsarki da suka jima kuma wannan wani mataki ne na ajiyar kayan tarihi na musulmi da wani abubuwa na tarihin musulmi a kasar da kuma zai zama mafi girma a yankin.
2012 Feb 19 , 16:56
Bangaren kasa da kasa; cibiyar da ke kula da addinin musulunci a Britaniya ta kaddamar da wata bazarar karatu da koyar da karatun kur'ani mai girma da hukumce-hukumce na musulunci ga wadanda bas u jima da karbar addinin musulunci a birnin London fadar mulkin kasar.
2012 Feb 19 , 16:55
Bangaren harkokin kur'ani : an fassara kur'ani mai girma a cikin harsunan Farisanci Da Peshtu gay an makaranta dake daukan karatu a matakin tsakatsakiya kuma cibiyar kula da karatunkur'ani ta balal a jamhuriyar musulunci ta Afganistan ta dauki dawainiyar tarjama wannan littafi a cikin wadannnan harsuna biyu masu muhimmanci a wannan kasa.
2012 Feb 16 , 17:48
Bangaren kur’ani, an sanar da sunan sakataren kwamnitin shiray gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta kasa da kasa ta Daliban jami’a na kasashen musulmi wadda za a gudanar a karo na hudu a jamhuriyar musulunci ta Iran.
2012 Feb 15 , 18:32
Bangaren kasa da kasa: a yau ne sha tara ga watan bahmain na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya karkashin himmar ma'aikatar da ke kula da harkokin addinin musulunci a kasar Katar za ta bude wata kungiya ta duniya da za ta rika gudanar da nazari da bincike a cikin kur'ani mai girma.
2012 Feb 08 , 14:29
Bangaren harkokin kur'ani mai girma: cibiyar kula da al'adun jamhuriyar musulunci ta Iran a birnin Delhu No na kasar Indiya a daidai lokaci guda na fara makon hadin kai a tsakanin musulmi ta shirya gasar karatun kur'ani mai girma da harda a fadin kasar ta Indiya daga ranekun sha bakai zuwa sha tara ga watan Bahman na shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya karkashin sa idon wakilin hukumar kula da al'adun jamhuriyar musulunci ta Iran a wannan kasa.
2012 Feb 07 , 15:01
Bangaren harkokin kur'ani : mai bada shawara kan harkokin kur'ani a hukumar kula da al'adu da dangantaka ta musulunci a jamhuriyar musulunci ta Iran ya bada labarin gudanar da wani mako na karatun Kur'ani mai tsarki a kasashe daban daban a dalilin zagayowar ranar haifuwar fiyayyan halitta ma'aikin Allah Muhammad dan abdullahi tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da alayan gidansa tsarkaka da kuma zagayowar kwanaki goma na nasarar juyin juya halin musulunci ta Iran.
2012 Feb 05 , 17:44
Bangaren kasa da kasa:a karo na shidda a garin karbala mai tsarki za a gudanar da taron baje kolin abubuwa da suka shafi kur'ani mai tsarki da abubuwan addini da aka bawa taken rabi'ul Risala wato damunar sakon annabci kuma ana gudanar das hi a daidai wannan lokaci na zagayowar ranekun tunawa da ranar haifuwar ma'aikin Allah tsira da amincin Allah ya tabbata a gare shi da kuma alayan gidansa da kuma Imam Jafar Sadik (AS).
2012 Feb 02 , 16:25
Bangaren adabi: babban darekta mai kula da harkokin hulda da jama'a a markadin Imam Rida (AS) ya bada labarin raba kur'anai dubu biyar ga baki wadanda ba Iraniyawa da suka ziyarci wannan guri mai albarka a cikin kwanaki goma na alfijir din nasarar juyin juya halin musulunci .
2012 Feb 02 , 16:24
Bangaren kasa da kasa; a karo na uku za a gudanar da gasar karatun kur'ani mai girma da harda a fadin hadeddiyar daular larabawa a gasar da aka bawa sunan kyautar kur'ani ta Khalifa bin Jabir da kuma za a fara a ranar shida ga watan Bahman na wannan shekara ta dubu daya da dari uku da tis'in hijira shamsiya.
2012 Jan 21 , 15:39
Bangaren kasa da kasa; Komandan hadin guiwar sojojin tarayyar Nigeria JTF ya karyata labarin da ake yadawa a yan kwanakin nan wai wani daga cikin sojojin kasar ta Nigeria ya wulakanta kur'ani mai girma.
2012 Jan 18 , 17:42