IQNA

Gasar Karatu Da Hardar Kur’ani Ta Daliban Sakadandare A Kasar Uganda

22:05 - June 15, 2021
Lambar Labari: 3486014
Tehran (IQNA) an gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta daliban sakandare a birnin Kampala na kasar Uganda.

Kamfanin dillancin labaran iqna daga birnin Kampala na kasar Uganda ya bayar da rahoton cewa, a jiya aka kammala gudanar da gasar karatu da hardar kur’ani mai tsarki ta daliban sakandare a kasar ta Uganda, tare da halartar dalibai fiye da 50.

A yayin gudanar da gasar dai wasu daga cikin jami’an gwamnati da wakilan wasu cibiyoyi na addini gami da wakilan wasu kafofin yada labarai na kasar at Uganda sun halarci wurin.  

Shugabar bangaren tsare-tsare na gasar Farida Ali Kolumba ta bayyana a karshen gasar cewa, wannan yana daga cikin ayyukan da suke tsarawa domin karfafa gwiwar matasa musulmi kan lamarin addini da kuma koyarwa ta kur’ani mai tsarki.

Ta ci gaba da cewa, abu ne da yake da matukar muhimmanci a cikin lamarin zamantakewar usulmi a duk inda suke, su tarbiyantar da ‘ya’yansu a kan tarbya ta kur’ani, wannan shi ne babban abin da zai zama shamaki ga gurbacewar tarbiyar matasa musulmi.

Daga karshe an bayar da kyautuka ga dukkanin wadanda suka shiga cikin gasar, da kuma wasu kyautuka na musamman ga wadanda suka fi nuna kwazo a  gasar, musamman wadanda suka zoa  matsayi na daya, da na biyu da kuma na uku.

3977567

 

 

captcha