IQNA

Morocco: An Kaddamar Da Kamfe Na Neman A Kori Wakilin Isra'ila

23:40 - June 06, 2021
Lambar Labari: 3485987
Tehran(IQNA) an kaddamar da wani kamfe na neman a kori wakilin Isra'ila daga kasar Morocco

Jaridar Quds Al-rabi ta bayar da rahoton cewa, dubban mutanen kasar Morocco ne suka shiga cikin wani kamfe na neman a kori shugaban ofishin wakilci na Isra'ila da ke kasar ta Morocco.

Rahoton cewa, wasu masu fafutuka ne suka kaddamar da kamfe din a shafukan sada zumunta na yanar gizo, wanda kuma ya samu karbuwa matuka  atsakanin mutanen kasar.

Wannan kamfe dai an kaddamar ad shi ne bayan yakin da Isra'ila ta kaddamara  kan al'ummar Gaza a cikin 'yan makonnin da suka gabata.

Morocco dai tana daga cikin kasashen larabawa da suka kulla alaka da Isra'ila, biyo bayan matsin lambar da gwamnatin Ammurka ta yi a kansu.

 

3975787

 

Abubuwan Da Ya Shafa: morocco kori jakadan
captcha