Jaridar The National News ta kasar Burtaniya ta bayar da rahoton cewa, kungiyar musulmi ta The Muslim Arts and Culture Festival a kasar Burtaniya da ke gudanar da ayyukan jin kai da taimako ta samu lambar yabo daga sarauniyar kasar ta Burtaniya.
Sakatariyar ma'aikatar kula da harkokin zamantakewar al'ummar kasa a Burtaniya Barones Barran ta bayyana cewa, an bayar da wannan kyauta ne ga wannan kungiya, saboda gagarumar gudunmawar da ta bayar wajen taimakon jama'a a lokacin da cutar corona ta yi tsanani a kasar.
Wannan cibiyar dai tana gudanar da ayyukanta ne a birnin Manchester, wanda shi ne birnin na uku mafi girma a kasar Burtaniya.
Daga cikin ayyukan da wannan cibiya take gudanarwa har da taimaka ma marassa karfi da abubuwan bukatar rayuwa, taimaka musu a asibitoci, kamar yadda kuma tana shirya taruka na wayar da kai domin kawp karshen nuna wariyar launin fata, ko kin jinin musulmi da dai sauransu.