IQNA

Ba Za A Gudanar Da Trukan Ranar Ghadir A Hubbaren Alawi Ba

21:24 - August 03, 2020
Lambar Labari: 3485049
Tehran (IQNA) cibiyar da ke kula da lamurran hubbaren Imam Ali A Najaf ta sanar da cewa a wanann shekara ba za a gudanar da tarukan ranar Ghadir a wannan hubbare ba.

Kamfanin dillancin labaran Saumaria News ya bayar da rahoton cewa, cibiyar da ke kula da lamurran hubbaren Imam Ali A Najaf Ashraf ta sanar da cewa a wanann shekara ba za a gudanar da tarukan ranar Ghadir a wannan hubbaren ba kamar yadda aka a kowace shekara.

Bayanin ya ci da, an dauki wannan matakin ne sakamakon yanayin da aka samu kai a wannan lokaci na bullar cutar corona, domin kare lafiya dukkanin mumiminai maso Amirul muminin daga kamuwa da wannan cuta wadda take yaduwa, ya zama wajibi a dauki irin wannan mataki.

Daga karshe bayanin ya nemi afuwar dukkanin wadada suka yi niyyar halartar wadannan taruka a shekarar bana.

A birnin karbala ma an bayar da sanarwar cewa an dakatar da duk wasu taruka daga nan har zuwa bayan 13 ga watan Muharram.

 

3914297

 

 

 

 

captcha