IQNA

Gidan Radiyon Kur’ani A Masar Ya Nemi Gafara Kan Watsa Kiran Salla Kafin Lokaci

21:29 - August 01, 2020
Lambar Labari: 3485044
Tehran (IQNA) gidan radiyon kur’ani na kasar Masar ya nemi uzuri daga jama’a kan kuren da ya yi wajen saka kiran sallar magariba kafin lokacin,

Gidan radiyon kur’ani na kasar Masar ya nemi uzuri daga jama’a kan kuren da ya yi wajen saka kiran sallar magariba kafin lokacin, wanda hakan ya faru ne a ranar alhamis da wasu suke azumin ranar arafa, inda kuma an saka kiran sallar ne mintuna 4 kafin lokacin.

A cikin bayanin da gidan radiyon ya fitar, ya nemi gafara daga al’umma kan wannan babban kure da aka samu, wanda a cewar bayanin ba a taba samun kure irin wannan ba a wannan gidan radiyo cikin tsawon shekaru fiye da hamsin, kuka za a gudanar da bincike domin musabbabin faruwar lamarin.

Bayan kiran sallar dai jama’a da dama da suke yin azumi sun yi buda baki, sai daga bisani aka lura cewa lokacin bai yi ba, amma babbar cibiyar bayar da fatawa ta kasar ta fitar da bayani da ke cewa, duk wadanda suka yi buda baki bayan jin wannan kiran salla bisa kure, azuminsu ya yi daidai.

 

 

3913845

 

 

 

 

captcha