IQNA

Cece Ku Ce A Kan Rusa Wani Wuri Na Tarihi A Masar

19:23 - July 30, 2020
Lambar Labari: 3485036
Tehran (IQNA) ana cece ku ce a shafukan zumunta  akan shirin gwamanati na rusa wani wurin tarihi a birnin Alkahira domin gina gada.

Shafin yada labarai na arab news ya bayar da rahoton cewa, sakamakon wani shirin gwamnati na gina wata babbar gada da za ta ratsa a cikin wata tsohuwar makabarta a cikin alkahira, ana ta cece ku ce a shafukan zumunta  a kan wannan shiri.

Bayanin ya ci gaba da cewa, an kaddamar da wani kamfe yanzu haka a shfukan sada zumunta musammana  facebook domin kalubalantar wannan shiri na gwamnatin kasar Masar.

Hesham Auf daya ne daga cikin masana lamarin tarihi a kasar Masar ya bayyana cewa, an saka wannan makabarta da aka gina sama da karni biyar da suka gabata a cikin wuraren tarihi na duniya a 2009, saboda haka rusa wannan wuri ya saba wa dokoki na duniya.

Sai dai Usama Tal’at shugaban bangaren gudanar da bincike kan wuraren tarihi a jami’ar Egypt-Japan University of Science and Technology, ya bayyana cewa abin da ake yadawa ba gaskiya ba ne, wannan wuri baya daga cikin wuraren tarihi na duniya.

 

3913384

 

captcha