IQNA

Sakon Jagora A Yayin Ayyukan Hajjin Bana

Muna Yin Allawadai Da Dabi'ar Wariya A Amurka Kuma Muna Goyon Bayan Mutane

20:54 - July 29, 2020
Lambar Labari: 3485032
Tehran (IQNA) kamar kowace shekara ajagoran juyin juya halin muslunci a Iran Ayatollah sayyid Ali Khamenei ya aike da sakonsa a daidai lokacin da ake gudanar da aikin hajjin bana.

Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Кai

 

Dukkan godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin talikai. Tsira da amincin Allah su tabbata ga (Annabi) Muhammadu da Alayensa tsarkaka da zaɓaɓɓun sahabbansa da waɗanda suka bi su cikin kyautatawa har zuwa ranar tashin alƙiyama.

 

Aikin hajji wanda a koda yaushe ya kasance wani lokaci ne na jin ɗaukaka, girma da kuma ci gaban duniyar musulmi, to sai dai a wannan shekarar muminai suna cikin damuwa da baƙin cikin rabuwa da juna. Zukata suna cikin kaɗaitaka sakamakon kaɗaitakar da Ka’aba take ciki, haka nan hawaye suna zuba sakamakon rashin samun damar amsa kiran Ubangiji. Wannan rashin na ƙaramin lokaci ne kuma da yardar Allah Maɗaukakin Sarki ba abu ne da zai jima ba. To sai dai darasin da ke cikin hakan shi ne fahimtar irin girman ni’imar da ke cikin aikin hajjin wanda dole ne a kiyaye hakan da kuma nesantar gafala daga hakan. Wajibi ne a wannan shekarar sama da kowane lokaci mu fahimci cewa sirrin girma da ɗaukakar al’ummar musulmi suna cikin haɗuwar muminai waje guda a haramin Ka’aba da na Annabi (s.a.w.a) da Imaman Baƙi’a (a.s) sannan kuma mu yi tunani kan hakan.

Aikin hajji wata farilla ce maras tamka; kana kuma abin alfahari tsakanin farillan Musulunci; da ke bayyanar da wajibcin dubi cikin dukkanin lamurra na ɗaiɗaiku da na al’umma, na ƙasa da sama, na tarihi da na addini. Akwai ababe masu kusanta mutum da Ubangiji a cikinsa, to sai dai kuma ba tare da an yi watsi da ababen duniya da kuma komawa gefe ba. Akwai taron al’umma a cikinsa, sai dai ba tare da rikici da tada jijiyoyin wuya ba. A ɓangare guda ga ababe masu ƙarfafa ruhi kama daga munajatoci da ambato (zikirin) Ubangiji, a ɓangare guda kuma ga haɗuwar zukata da taruwa ta jama’a. Mahajjati ta wani ɓangaren yana sake sabunta tsohuwar alaƙar da ke tsakaninsa da tarihi ne – tare da Ibrahim da Isma’il da Hajar, da Manzon Allah yayin da yake shiga Masjid al-Haram cikin nasara, tare da dubun dubatan muminan farkon Musulunci – sannan da ɗaya idon kuma yana kallon miliyoyin muminan zamaninsa wanda kowane guda daga cikinsu yana iya zama wani hannun da za su haɗu da juna wajen riƙo da igiyar Allah.

Tunani da kuma dubi cikin aikin hajji, za su iya sanya mahajjati yarda da cewa matuƙar ba a samu haɗin kai da aiki tare a tsakanin ma’abota addini ba, to kuwa ba za a iya cimma da dama daga cikin koyarwa da kuma fata na addini ga ɗan’adam ba, sannan kuma idan aka sami irin wannan haɗin kai da aiki taren, to kuwa kaidin maƙiya da masu fatan sharri ba za su zamanto wata matsala mai muhimmanci a kan tafarkin su ba.

Aikin hajji, wani atisaye da tabbatar da ƙarfi ne a gaban ma’abota girman kai waɗanda su ne tushen fasadi da zalunci da babakere da satar dukiyar raunana, sannan a halin yanzu kuma jiki da rayukan al’ummar musulmi cike suke da irin waɗannan zalunci da babakeren waɗannan mutanen. Aikin hajji, wata alama ce da ke nuni da irin ƙarfi da ƙwarewar da al’ummar musulmi suke da ita a yanzu da kuma nan gaba. Wannan shi ne dabi’ar hajji da ruhin hajj kana kuma wani ɓangare mai muhimmanci na manufar hajji; wannan kuma shi ne abin da marigayi Imam Khumaini mai girma ya kira shi da ‘hajjin Annabi Ibrahim. Idan da masu kula da ayyukan hajjin waɗanda suke kiran kansu da sunan masu hidima wa haramomi biyu, idan da sun sauke wannan nauyi da gaske, sannan maimakon neman yardar gwamnatin Amurka, suka tsaya wajen neman yardar Allah, da sun sami damar magance manyan matsalolin duniyar musulmi.

A halin yanzu kamar kullum kai sama da hakan ma, maslaha ta wajibi ta al’ummar musulmi tana cikin haɗin kansu ne; haɗin kan da zai haifar da aiki tare tsakanin musulmi wajen tinƙarar barazana da ƙiyayyar da ake fuskanta, sannan da kuma tinƙarar mutum-mutumin shaiɗan, Amurka ma’abociyar wuce gona da iri da ‘yar kwuikuyonta gwamnatin sahyoniyawa sannan kuma a tsaya ƙyam wajen faɗa da dukkanin masu tinƙaho da ƙarfi (na duniya). Wannan shi ne ma’anar umurnin Allah  da ke cewa: “Kuma ku yi riƙo da igiyar Allah gaba ɗaya kuma kada ku rarraba([1]).”, Alƙur’ani mai girma yana gabatar da al’ummar musulmi da cewa Masu tsanani ne a kan kafirai, masu rahama ne a tsakaninsu([2]), sannan kuma ya buƙace su da “Kuma kada ku karkata zuwa ga waɗanda suka yi zalunci([3])” “Kuma Allah ba Zai sanya hanya ga kafirai a kan muminai ba([4])”, “To ku yaƙi shugabannin kafirci([5])”, “Kada ku riƙi maƙiyiNa kuma maƙiyinku masoyi([6]), sannan kuma don su gane maƙiya, sai ya fitar musu da hukuncin “Allah ba Ya hana ku, daga waɗanda ba su yaƙe ku ba saboda addinin kuma ba su fitar da ku ba daga gidajenku([7]). Lalle har abada bai kamata mu musulmi mu yi watsi da kuma mantawa da waɗannan umurni masu muhimmanci da kuma ayyana makoma daga tunaninmu ba.

A yau sama da shekarun baya al’umma da masana da masu kishin cikinmu muna da ikon samar da wannan sauyi. A yau farkawa irin ta Musulunci da ma’anar dawowar hankulan masu faɗi a ji da kuma matasan musulmi zuwa ga irin ƙarfi na ruhi da na zahiri da ake da shi wanda kuma wani abu ne da ba za a iya inkarinsa ba. A yau tsarin jari hujja da gurguzu waɗanda shekaru ɗari ko shekaru hamsin ɗin da suka gabata ake ganinsu a matsayin tushen ci gaban ƙasashen yammaci, sun faɗi ƙasa warwas sannan kuma aibin da ke tattare da su sun fito fili ga kowa. Tushen da na farkon ya ginu kansa ya faɗi ƙasa warwas, haka nan tushen da na biyun ya ginu a kai shi ma a halin yanzu yana fama da manyan matsaloli, kuma yana hanyar faɗuwa.

 

A halin yanzu ba wai kawai tsari da salon al’adu na ƙasashen yammaci – wanda tun da fari ma ya ginu ne bisa tushen wauta da abin kunya – ba hatta tsarinsa na siyasa da tattalin arziki, wato tsarin demokraɗiyyar da ya ginu bisa dukiya da jari hujja da nuna wariya, gazawa da kuma fasadin da ke cikinsa a fili sai ƙara bayyana yake yi.

A halin yanzu akwai wani adadi mai yawa na masana a duniyar musulmi waɗanda cikin alfahari suke kalubalantar dukkanin ikirarin da ci gaban yammaci yake yi da kuma gabatar da tsarin Musulunci a matsayin makwafinsu. A halin yanzu hatta wasu masanan ƙasashen yammaci da suke alfahari da tsarin yammacin da kuma bayyanar da shi a matsayin tushen duk wani ci gaba, yanzu ya zama dole suka janye wannan magana ta su da kuma amincewa da gazawar da suka yi a

fagen fahimta da kuma ilimi. Dubi cikin titunan Amurka da irin mu’amalar da ‘yan siyasar Amurkan suke yi da al’ummar su, da irin tsananin bambancin da ke tsakanin al’ummar ƙasar, da irin wauta da rashin sanin ya kamatan jami’an ƙasar da aka zaɓa, da irin gagarumin nuna wariyar launin fatan da ke gudana a ƙasar, da irin rashin imanin da jami’an tsaron ƙasar suke nunawa kan wani mutum da ba a same shi da laifi da yadda suka azabtar da shi a gaban idanuwan masu wucewa kana da kuma kashe shi, dukkanin waɗannan wasu abubuwa ne da suke nuni da irin tsananin matsalar kyawawan halaye da zamantakewa da ci gaban yammaci yake fuskanta da kuma rashin inganci tunaninsa na siyasa da tattalin arziki. Mu’amalar Amurka da raunanan al’ummomi, ita ce dai irin mu’amalar ɗan sandan nan da ya sanya gwiwarsa a wuyan wani baƙin fata maras kariya sannan ya dinga matse shi har da ya kashe shi. Su ma sauran gwamnatocin ƙasashen yammaci kowace guda gwargwadon iyawarta, haka suke.

Aikin hajji irin na Annabi Ibrahim, wani salo ne na irin ci gaban Musulunci a gaban tsarin jahiliyya na zamani. Aikin hajji kira ne zuwa ga Musulunci kana kuma alama ta irin kyawun tsarin zamantakewa na al’ummar musulmi. Al’ummar da a cikinta ake iya ganin rayuwa tare tsakanin muminai da kuma taruwa ƙarƙashin inuwar tauhidi. Nesantar duk wani rikici da karo da juna, nesantar duk wani nuna wariya da fifita wasu, nesantar fasadi da lalacewa a matsayin sharaɗin hakan. Jifan shaiɗan da barranta daga mushirikai, ƙulla alaƙa da talakawa, taimakon marasa shi da kuma ɗaga taken  imani, suna daga cikin nauyi na wajibi da ke wuyan musulmi. Kana kuma da tabbatar da maslaha da manufofi na gaba ɗayan al’umma tare da ambato da gode wa Allah da bayinsa, a matsayin babbar manufar wannan aikin. Wannan ita ce alama ta gaba ɗaya ta al’ummar musulmi cikin aikin hajjin Annabi Ibrahim. Ko shakka babu kwatanta hakan da irin halin da al’ummomin ƙasashen yammaci suke ciki wani lamari ne da zai sanya zuciyar kowane musulmi ma’abocin himma cikin shauƙi da kuma ƙoƙari wajen isa ga irin wannan al’umma.

Mu al’ummar Iran ƙarƙashin shiryarwa da kuma jagorancin Imam Khumaini, mun aiwatar da wannan yunƙuri kuma mun yi nasara. Ba ma ikirarin cewa mun cimma abin da muka sani sannan kuma muke son tabbatar da shi a lokaci guda, to amma muna ikirarin cewa lalle mun ci gaba a wannan tafarkin sannan kuma mun kawar da matsaloli da dama da suke bisa wannan tafarkin. Albarkacin imani da alƙawarin Alƙur’ani, lalle ƙafafunmu sun tsaya ƙyam. Babbar shaiɗaniyar wannan zamani kana ma’abociyar shan jini wato gwamnatin Amurka ta gaza wajen razanar da mu ko kuma ta sanya mu faɗawa tarkon makircinta ko kuma ta hana mu samun ci gaba na duniya da kuma lahira.

Mu dai muna ɗaukar dukkanin al’ummar musulmi a matsayin ‘yan’uwanmu ne, haka nan muna mu’amala da waɗanda ba musulmin da ba su shiga cikin sahun maƙiya ba, mu’amala ta kyautata da adalci. Muna ɗaukar damuwa da baƙin cikin al’ummar musulmi a matsayin damuwa da kuma baƙin cikinmu, sannan kuma muna ƙoƙari wajen magance hakan. A kullum muna sanya taimakon al’ummar Falasɗinu da ake zalunta, nuna damuwa da halin da al’ummar Yemen suke ciki da dukkanin musulmin da suke ƙarƙashin zalunci a duk inda suke a duniya a matsayin lamarin da muke ba shi muhimmanci a ko yaushe. Muna ganin yin nasiha ga wasu shugabannin ƙasashen musulmi a matsayin wani nauyin da ke wuyanmu; su kuwa ‘yan siyasar da maimakon su dogara da ‘yan’uwansu musulmi, suka koma ga neman taimakon maƙiya da kuma ƙasƙantar da kansu da kuma yarda da shiftar maƙiya da ƙasƙantar da al’ummomin su – waɗanda suka yarda da ci gaba da wanzuwar azzalumar gwamnatin sahyoniyawa ‘yar fashin ƙasa, sannan a fili da kuma a ɓoye suke nuna abokantakarsu da ita – don samun wani ɗan amfani na ƙaramin lokaci, muna musu nasiha da kuma jan kunnensu dangane mummunan sakamakon wannan aiki na su. Kasantuwar Amurka a yankin Yammacin Asiya wani lamari ne mai cutarwa ga al’ummomin yankin da kuma tabbatar da rashin tsaro da kuma koma bayan ƙasashen da ke wajen. Dangane da abin da ke faruwa a halin yanzu a Amurka na irin yunƙurin nuna ƙyamar nuna wariyar launin fata a wajen kuwa, toh matsayar mu dai ita ce goyon bayan al’umma da kuma yin Allah wadai da irin wannan mu’amala ta rashin imani da nuna wariya ta gwamnatin ƙasar.

Daga ƙarshe yayin da na ke miƙa gaisuwa da kuma sallamata ga mai girma Baƙiyatullah (rayukanmu su zamanto fansa a gare shi), ina jinjinawa ambaton marigayi Imaminmu mai girma sannan kuma ina miƙa sallama ta ga ruhin shahidai ina kuma roƙon Allah Maɗaukakin Sarki da Ya tabbatar mana da aikin hajji cikin tsaro kana kuma karɓaɓɓe ga al’ummar musulmi.

 

Amincin Allah Ya tabbata ga bayinSa salihai.

 

Sayyid Ali Khamenei

 

7/5/1399

7, Zul Hajj 1441.

3913419

 

captcha