IQNA

Keta Alfarmar Kur’ani A Tunisia Ya Jawo Tayar Da Jijiyoyin Wuya

22:59 - May 06, 2020
Lambar Labari: 3484769
Tehran (IQNA) sakamakon keta alfarmar kur’ani da wata budurwa ‘yar kasar Tunisia ta yi a shafukan zumunta hakan ya jawo fushin al’ummar kasar.

Shafin alwatan ya bayar da rahoton cewa,a  cikin shafinta na zumunta budurwar ta saka wata aya ta jabu ta kuma danganta hakan da kur’ani.

Wannan lamari ya sanya jama’a a kasar yin kira ga mahukunta da  adauki matakin gaggauwa domin ladabtar da wannan yarinya kan abin da ta aikata na keta alfarmar kur’ani mai tsarki.

Tuni kotun kolin kasar Tunisia ta bayar da umarni aka kame yarinya, kuma an fara gudanar da bincike a kana bin da ta aika bisa tuhumar wulakanta addinin muslunci.

Sai dai a nata yarinyar ta musunta cewa ta yi haka ne domin wulakanta addini, domin ita kanta musulma ce, kuma ba ta ambaci wani daga cikin abubuwa masu tsarki na addini a cikin abin da yada ba.

3897073

 

captcha