IQNA

An Sake Gano Wani Wani Wurin Horar Da Mutane A Kaduna Najeriya

23:01 - October 20, 2019
Lambar Labari: 3484174
Bangaren kasa da kasa, an sake gano wani wuri da ake horar da kangararru a cikin jihar Kaduna.

Kamfanin dilalncin labaran iqna ya nakalto daga shafin Legit cewa,  yan sanda sun sake kai farmaki wata haramtacciyar cibiyar horar da kangararru a yankin Rigasa dake jihar Kaduna.

An tattaro cewa a wannan karon, gwamna Nasir El-Rufai ya kasance tare da jami’an tsaron a lokacin da suka kai farmaki haramtacciyar cibiyar dake karamar hukumar Igabi a jihar.

An ceto akalla mutane 147 tare da wasun su a daure daga cibiyar wanda aka fi sani da cibiyar horar da kangararru na Malam Niga’.

Daga cikin wadanda aka ceto akwai mata 22 da yan kasar waje hudu yayinda jami’an tsaro suka tafi da mai cibiyar don gudanar da bincike.

Daga karashe dai an kai wadanda lamarin ya cika dasu zuwa sansanin yan Hajji a a yankin Mando dake Babban birnin jihar don samun cikakkiyar kulawa.

A cewar gwamnatin, za a sada su da iyalensu idan aka kammala basu kulawa.

3851017

 

 

captcha