Kamfanin dillancin labaran iqn aya habarta cewa, kamfanin Iffah Hijab na kasar Malaysia, ya bayar da kyautar dinkakken hijabin lullubi ga mata musulmi dubu 10 a kasar.
Wanann na zuwa ane a lokacin da kamfanin ke bukin zagayowar cikar shekara guda da ya fara aiki a kasar.
Dukkanin hijaban da kamfanin ya bayar kyauta, masu tsada ne wadanda aka dinka su da siliki wanda ba kasafai yakan yi saurin lalacewa ba. Haka nan kuam kayan wannan kamfani sun samu karbuwa matuka a kasar da ma kasashen musulmi.