IQNA

Jam’an Tsaron Morocco Sun Rusa Wani Gungun ‘Yan Ta’adda

18:59 - January 23, 2019
Lambar Labari: 3483327
Bangaren kasa da kasa, jami’an tsaron kasar Morocco sun rusa wani gungun ‘yan ta’adda a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna, tashar Sky News ta bayar da rahoton cewa, a jiya jami’an tsaron kasar Morocco sun kai samame a wata maboyar ‘yan ta’adda a yankin Kazablanka.

Baynin jami’an tsaron ya ce an kai samamen ne bayan samun cikakkun bayanai kan wuraren da ‘yan ta’addan suke byewa ne, kuma an kame 13 daga cikinsu.

Haka nan kuma an samu tarin makamai a wurin da suka hada da bindigogi da kuma wasu kayan hada abubuwa masu tarwatsewa.

Kasar Morocco dai na daga cikin kasashen larabawan arewacin Afrika, wadanda suke da yawan ‘yan ta’adda da suke kai hare-hare a cikin kasashen siriya da sunan jihadi.

3783919

 

captcha