IQNA

Sudan: Jami'an Tsaro Sun Kame 'Yan Jarida 38

23:23 - January 19, 2019
Lambar Labari: 3483325
Jami'an tsaron gwamnatin Sudan sun kame 'yan jarida 38 bisa zarginsu da bayar da rahotanni masu tunzura jama'a.

kamfanin dillancin labaran iqna, ya bayar da rahoton cewa, jami'an tsaron gwamnatin kasar ta Sudan ta kame 'yan jaridar 38 ne bisa tuhumar cewa rahotannin da suke bayarwa ba na gaskiya ba ne, kuma suna tunzura jama'a ne wajen kara fitowa kan tituna domin nuna kyama ga gwamnati.

Daga cikin mutanen 28 suna aiki ne da tashoshin radiyo da talabijin da kuma jaridu, yayin da 10 daga cikinsu kuma suna aiki ne a kafofin yada labarai ta hanyoyin sadarwa na yanar gizo.

Yanzu haka dai ana tsare da su a babban gidan kaso da ke birnin Khartum, inda za a gurfanar da su a gaban kulya, bisa tuhumar yada labaran karya.

Sai dai a daya bangaren kungiyoyin kare hakkin bil adama da na 'yan jarida a kasar ta Sudan sun soki lamirin gwamnati kan wanann lamari, inda suke bayyana hakan da cewa yunkuri ne na rufe bakunan 'yan jarida daga bayyana hakikanin abin da yake faruwa a kasar.

Al'umar Sudan suna gudanar da bore tun tsawon makonni 5 ad suka gabata ne domin nuna rashin aincewarsu da tsadar rayuwa  akasar, inda daga bisani kuma suke kira ga shugaban kasar Umar Albashir

wanda ya yi shekaru 30 yana mulki a kasar da ya sauka.

3782312

 

captcha