IQNA

Kur’ani Mai Shekaru 1000 A Kasar Aljeriya

20:15 - January 17, 2019
Lambar Labari: 3483320
Bangaren kasa da kasa, an nuna wani kwafin kur’ani mai tsarki da ake danganta shi da shekaru 1000 da suka gabata a garin Khanshala.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai Amasa ya bayar da rahoton cewa, a baje kolin kayan tarihi da ke gudana  a lardin Khanshala a kasar Aljeriya, an nuna wani kwafin kur’ani mai tsarki da ake danganta shi da shekaru 1000 da suka gabata.

Wanda yake mallakar wannan kwafin kur’ani ya bayyana cewa, sun gaje shi ne tun kaka da kankanni, kuma kur’anin yana nan tun lokacin hijirar Amazigawa daga yankin Saqiyyah Hamra.

3781761

 

 

 

captcha