IQNA

ISESCO Ta Yi Allawadai Da Isra’ila

23:54 - January 15, 2019
Lambar Labari: 3483315
Bangaren kasa da kasa, kungiyar bunkasa harkokin ilimi da ala’adu ta kasashen musulmi ta yi Allawadai da Isra’ila kan tozarta wuraren tarihi na Palastine.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, kamfanin dillancin labaran UNA ya bayar da rahoton cewa, a cikin wani bayani da ta fitar jiya, kungiyar bunkasa harkokin ilimi da ala’adu ta kasashen musulmi ISESCO ta yi Allawadai da Isra’ila kan bata wuraren tarihi na Palastine da take yi.

Bayanin ya cea  cikin ‘yan lokutan nan Isra’ila ta rusa wuraren tarihi da dama da suke da alaka da addinin muslucni da kuma tarihin Palastine a cikin birnin Quds da kewaye, wanda a cewar bayanin wannan sabawa dukkanin yarjeniyoyi na duniya kan kiyaye wuraren tarihi.

Kungiyar ta ce za ta dauki matakin kai kara kan wannan lamari, domin tabbatar da cewa an ladabtar da Isra’ila kan wannan aika-aika da take yi a kan wuraren tarihin musulmi da na larabawa da ke Palastine.

A baya-bayan nan dai Isra’ila ta rusa wasu muhimman wurare na tarihi na muuslmi da aka gina su tun shekaru 1200 da suka gabata, kamar yadda kuma take ci gaba da gina ramuka  akarkashin masallacin quds, wanda hakan zai iya sanya masallacin rufta.

3781660

 

 

 

 

captcha