Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Usman Domble dan wasan kasar Faransa da ke awasa Barcelona wanda dan asalin kasar Mauritaniya ne yana shirin gina masallaci a a yankinsu.
Dan wasan ya bayyana hakan ne bayan kammala wasan cin kofin kwallon kafa na kasashen duniya ne a kasar Rasha wanda kasar ta Faransa ta dauki kofin.
Ya bayyana cewa babban abin arin ciki ne a gare shi ya gina masallaci a mahaifarsa da ke cikin kasar Mauritaniya.
An tafi da shi kasar Faransa ne tun yana karamin bayan da mahaifiyarsa ta yi hijira zuwa Faransa.