IQNA

Babban Mai Bada Fatawa A Australia Ya Rasu

22:51 - July 11, 2018
Lambar Labari: 3482826
Bangaren kasa da kasa, Sheikh Abdulazim Alafifi babban mai bayar da fatawa na kasar Australia ya rasu a birnin Malburn.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, shafin yada labarai na IPP ya habarta cewa, Sheikh Afifi ya kasance daya daga cikin manyan limamai na kasar Australia, kuma a cikin watan Maris na wannan shekara aka zabe shi a matsayin babban mai bada fatawa ga musulmi na kasar.

Babbar majalisar muuslmin kasar Australia ta fitar da sanarwar taaziyya ga dukkanin musulmin kasar kan wannan babban rashi.

A cikin bayanin an bayyana shi matsayin mutumin da ya kwashe fiye da shekaru 20 yana hidima ga muuslmin kasar.

Robbin Scott ministan al’adu na kasar Australia ma ya fitar da bayanin ta’aziyya kan rashuwar sheikh Afifi.

Akwai muuslmi kimanin dubu 600a  kasar Australia, wato kimanin kashi 3 cikin dari na dukkanin al’ummar kasar.

3729126

 

 

captcha