IQNA

Tattaunawar Mabiya Addinan Musulunci Da Kiristoci A Najeriya

22:07 - July 10, 2018
Lambar Labari: 3482822
Bangaren kasa da kasa, karamin ofishin jakadancin kasar Iran zai dauki nauyin shirya wani taro na kara kusanto da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai a Najeriya.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, karamin ofishin jakadancin kasar Iran a birnin Abuja zai dauki nauyin shirya wani taro na kara kusanto da fahimtar juna tsakanin mabiya addinai a Najeriya da suka hada da kiristoci da kuma musulmi.

Azimi Nasr Abad shugaban karamin ofishin jakadancin Iran a Najeriya ya bayyana cewa, babbar manufar hakan ita ce kara kusanto da fahimtar juna a tsakanin dukkanin al'ummomin Najeriya.

Jakadan na Iran ya ce hakika sun yi takaici matuka dangane rikcin baya-bayan na da ya faru, wanda jama'a da dama suka rasa rayukansu, tare da yin fatan samun dawwamen zaman lafiya tsakanin dukkanin al'ummomin najeriya da ma duniya baki daya.

A taron dai malamai daga dukkanin bangarori na addinin muslunci da kirista gami da masana duk za su gabatar da jawabi, inda za su kara yawo hankalin al'umma kan wajabcin zaman lafiya.

3728875

 

 

 

 

 

 

captcha