IQNA

Isra'ila Ta Ki Amincewa Da A Shigar Da Gawar Mahardacin Kur'ani Da Ta Kashe

23:49 - April 22, 2018
Lambar Labari: 3482593
Bangaren kasa da kasa, ministan yakin haramtacciyar kasar Isra'ial ya ce ba yarda a shigar da gawar Fadi Batash a cikin Gaza ba.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, Liberman ministan yakin haramtacciyar kasar Isra'ial ya ce ba yarda a shigar da gawar Fadi Batash a cikin Gaza ba ta hanyar Rafah.

A jiya ne dai aka kasha fadi Batash wani masani kuma malamin jami'a dan palastinu kuma mahardacin kur'ani mai tsarki.

Wasu mutane da ba a san ko su wane ne ba suka kasha shi, amma tuni aka nuna yatsan tuhuma ga kungiyar liken asirin Isra'ila ta Mossad wadda ta saba gudanar da irin wadannan ayyuka na ta'addanci.

Shi ma a nasa bangaren shugaban kungiyar Hamas Isma'ila Habiyya ya bayyana cewa ko shakka babu wannan aikin Mossad ne.

3707801

 

 

 

 

 

 

captcha