Kamfanin dilalncin labaran iqna ya ahbarta cewa, ma'aikatar kiwon lafiya a yankin zirin gaza ta sheda cewa, a yau Juma'a Sojojin Isra'ila sun bude wutar bindiga akan palastinawa masu gangami da suke yin kira kan wajabcin dawo musu da hakkokinsu, da kuma bayar da dama ga sauran palastinawa da suka yi hijira da su dawo gida.
Rahotanni sun tababtar da cewa bayan ga shahadar palastinawa hudu a yau, wasu fiye da dari shida sun samu raunuka, kuma ana kula da wasu daga cikinsu a asibitoci daban-daban a zirin Gaza.
Tun daga ranar 30 ga watan maris din da ya gabata ne al'ummar Gaza suka fara gangamin yin kira kan hakkin dawowar palastinawa da Isra'ila ta kora daga yankunansu.