IQNA

Ana Shirin Fara Wani Shirin Bayar da Horo Kan Kur'ani A Senegal

23:49 - April 20, 2018
Lambar Labari: 3482589
Bangaren kasa da kasa, ana shirin fara gudanar da wani shirin bayar da horo kan kur'ani mai tsarki a kasar Senegal a birnin Dakar fadar mulkin kasar.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin kamfanin dillanin labaran Arabi INA cewa, hukumar bunkasa harkokin ilimi da aladu ta kasashen musulmi ISESCO na shirin fara gudanar da wani shirin bayar da horo kan kur'ani mai tsarki a birnin Dakar fadar mulkin kasar Senegal.

Bayanin y ace wannans hiri zai mai da hankali wajen bayar da horo kana bin da ya shafi karatu da kuma sanin kaidojin karatun kur'ani ta hanyoyi na zamani mafi sauki, ta yadda kuma malamai da suke koyarwa  amakarantu shirin zai shafa.

Baya ga haka kuma za akara wayar da kan malaman kan hanyoyin da za su domin tarbiyantar da dalibai kan hanyoyin koyon kur'ani da ma'noninsa ta hanyar da ta dace, da koma kaucewa duk wani abin da zai sanya yara daukar tsatsauran ra'ayi ta hanyar rashin fahimtar kur'ani.

3707212

 

 

 

captcha