IQNA

Gasar Kur’ani Ta Daliban Makaranta A Danmark

23:50 - April 19, 2018
Lambar Labari: 3482585
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da wata gasar karatun kur’ani ta daliban makarantun sakandare a yankin Glostrup da ke karkashin gundmar Kopenhag.

 

Kamfanin dillanci labaran iqna ya habarta cewa, a jiya ne aka gudanar da wata gasar karatun kur’ani ta daliban makarantun sakandare a yankin Glostrup da ke karkashin gundmar Kopenhag fadar mulkin kasar ta Denmark

Masallacin Fateh da ke karkashin cibiyar musulunci ta kasar wadda take kula da harkokin da suka shafi musulmi a kasar.

Wannan gasa dai an gudanar da ita ne da nufin kara karfafa gwiwar matasa muuslmi mazauna kasar kan harkokin da suka shafi kur’ani mai tsarki.

Ilyas Kukchi shugaban cibiyar hadin kan kungiyoyin muuslmi a kasar ya gabatar da jawabi a wajen taron rufe gasar, inda ya ce kur’ani mai tsarki shi ne ya hada dukkanin musulmi, kumariko da shin a nufin riko da igiya guda daya, wadda ita ce tafarkin nasar ga muuslmi, idan kuma suka yi watsi da shi to sun shiga dimuwa kenan.

3707010

 

 

 

 

captcha