Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, karamin ofishin jakadancin Iran a birnin Addis Ababa ya sanar da cewa, Abdulmajid Naser mahardacin kur'ani dan kasar ta Habasha ya kama hanyarsa ta isa Tehran domin halartar gasar kur'ani ta duniya karo na 35 da za a gudanar a kasar Iran.
A gobe ne dai za a bude gasar wadda babban masallacin marigayi Imam Khomenei da ke cikin birnin Tehran fadar mulkin kasar Iran, tare da halartar makaranta da mahardata kur'ani kimanin dari uku da saba'in daga kasashen duniya daban-daban.
3706687