IQNA

An Kame Wasu Daga Magoya Bayan Sheikh Zakzaky A Najeriya

23:47 - April 17, 2018
Lambar Labari: 3482578
Bangaren kasa da kasa, jami’an tsaron Najeriya sun kame wasu daga cikin magoya bayan sheikh Zakzaky a lokacin da suke gudanar da jerin gwanon kira da a sake shi.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga kamfanin dillancin labaran kasar Faransa cewa, a jiya jami’an tsaron Najeriya sun kame wasu daga cikin magoya bayan sheikh Zakzaky a lokacin da suke gudanar da jerin gwanon kira da a sake shi a birnin Abuja fadar mulkin kasar.

Rahoton ya ce an kame mutane kimanin 115, kuma an jikkata wasu da dama, inda yanzu haka ake kua da wadanda aka suka samu munanan raunuka.

Shugaban dandalin yada labarai na Harhar musulunci a Najeriya Malam Ibrahim Musa ya sheda wa kamfanin dillancin labaran AFP cewa, zaga-zangar da aka gudanar ba ta da bambanci da sauran wadanda suka gabace ta, sai dai a wanann karo jami’an tsaro sun dauki mataki yin amfai da karfi domin hana jerin gwanon.

A nasu bangaren jami’an tsaron Najeriya sun ce sun dauki matakin yin amfani da karfi domin tarwatsa zanga-zangar ne saboda ain da suka kira tayar da hankalin jama’a da ake yi.

Sai dai Malam Ibrahim Musa ya mayar da martani da cewa jerin gwanon baya tayar da hankalin kowa, domin kuwa tun da aka fara ba a taba jin cewa sun yi rigima da wani ba, ko a wannan karon jami’an tsaro ne da kansu suka kawo hari suka tayar da hankali da kawo yamutsi.

3706320

 

captcha