IQNA

An Nuna Makalar Wani Masani Dan Iran A Taron Ilimin Kur’ani A Tunisia

23:33 - April 15, 2018
Lambar Labari: 3482572
Bangaren kasa da kasa, an nuna makalar wani masani dan kasar Iran a matsayin daya daga cikin fitattun makaloli a taron kasa da kasa kan ilmomin kur’ani.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, a taron kasa da kasa kan ilmomin kur’ani a jami’ar Zaituna ta kasar Tunisia,  an nuna makalar wani masani dan kasar Iran a matsayin daya daga cikin fitattun makaloli a taron.

Wannan taro na kasa da kasa na samun halartar malamai da masaa daga kasashe daban-daban na duniya, kamar yadda aka gayyaci masani uku daga jami’ar Radhawi da kuma Firdausi daga Mashhad a kasar Iran.

Ali Akbar Rostomi shi ne shugaban bangaren nazarin ilmomi na jami’ar Radhawi, ya gabatar da wata makala kan ilmomin kur’ani mai tsarki a wurin taron, wadda aka bayyana ta a matsayin makala da ta kunshi dukkanin bangarori da ake bukatar bayani a kansu a wurin taron.

Jaafa alawi na daga cikin masana na kasa da suke halartar wannan taro, wanda ya gabatar da jawabi a wurin taron.

Daga cikin kasashen da suke halartar aron dai akwai Jordan, Libya, Iran, saudiyya, Algeriya, Morocco.

3705849

 

 

 

 

captcha