IQNA

Wani Malamin Yahudawa: Kafa Isra’ila Ya Sabawa Koyarwar Addinin Yahudanci

22:47 - January 23, 2018
Lambar Labari: 3482329
Bangaren kasa da kasa, Mir Hirush wani fitaccen malamin yahudawa ya bayyana cewa, abin da Isra’ila take yi ya sabawa koyarwar annabi Musa (AS).

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadrawa na sadal balad cewa, a cikin wata wasika da wannan malamin yahudawa ya aikewa babban malamin cibiyar Azahar ya bayyana cewa, suna goyon bayan taron da aka shirya a Masar mai taken Taimakon Quds.

Ya ci gaba da cewa, suna goyon bayan duk wani mataki wanda zai taimaka wajen kawo karshen tsarin yahudanci na Sahyuniya wanda Isra’ila ta ginu a kansa.

Dangane da mamayar yankunan Palastinawa da yaudawan sahyuniya suke yi kuwa, ya bayyana cewa babu wani wuri a cikin yahudanci da aka halasta zalunci da mamaya da kuma kwace kasar wani, saboda hakan abin da gwamnatin yahudawan Sahyuniya ke  yi a palastine baya cikin koyarwar attaura.

Haka nan kuma ya kirayi sauran al’ummomi musamman ma musulmi da kiristoci, da su gane cewa yahudawan sahyuniya ba suna kan koyarwar addinin yahudanci ba ne.

Wannan malamin yahudawa shi ne ya kafa wata kungiya da ake kira Natori, wadda take tsananin kiyayya da yahudawan sahyuniya, tare da kin Isra’ila da kuma zaluncin da take yi kan musulmi da larabawa.

3684633

 

 

captcha