IQNA

Musulmin Amurka Sun Nuna Rashin Amincewa Da Kalaman batunci Na Wani Jami’i

22:44 - January 23, 2018
Lambar Labari: 3482328
Bangaren kasa da kasa, babbar cibiyar musulmin kasar Amurka ta nuna rashin amincewa kan kalaman batunci da wani jami’in kasar ya yi kan musulmi da addinin musulunci.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na CAIR cewa, Couchnisky wani jami’i ne a garin Jackman cikin jahar Mine, wanda ya bayyana musulmi a matsayin mutane marassa kan gado masu kama da dabboi.

Wannan furuci ya fuskanci kakkausar suka da martani mai zafi daga cibiyar musulmin kasar ta Amurka, tare da bayyana hakan a matsayin babban abin takaici.

Cibiyar ta kara da cewa, kyamar musulmi ko baki ‘yan kasashen ketare a kasar Amurka an san hakan ne daga wasu ‘yan tsirarun mutane a lokutan baya, amma a yanzu a kasar Amurka tun bayan zaben da aka yi hakan ya zama matsayar gwamnati, kuma jami’an gwamnatin Amurka ne suka kara ruruta wutar kyamar musulmi a kasar a halin yanzu.

Bayanin cibiyar ya ce wannan furuciabin takaici ne, kuma ya dace a yi Allah wadaida hakan matukar dai ana fatan ganin Amurka ta ci gaba da wanzuwa  a matsayin kasa ta dimukradiyya.

A cikin makon da ya gabata ma an kori wasu malaman makaranta guda biyu a jahar Texas, saboda tsanin kyamar da suke nuna wa dalibai musulmi da suke karatu a karkashinsu.

3684627

 

 

captcha