IQNA

Taron Jami’an Tashoshin Kur’ani Na Duniya A Alkahira

22:42 - January 23, 2018
Lambar Labari: 3482327
Bangaren kasa da kasa, za a gudanar da taron jami’an gidajen radio na kur’ani na duniya karo na hudu a kasar Masar.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Ina cewa, wannan taron zai gudana ne a karkashin kulawar cibiyar kula da harkokin ilimi da al’adu ta kasashen musulmi ISESCO.

Babbar manufar gudanar da wannan taron dai ita ce ita samar da hanyoyi na gabatar da shirye-shirye na addini, wadanda za su taimaka wajen yi wa muuslmi musamman matasa saiti, domin kaucewa shiga kungiyoyin ‘yan ta’adda da sunan addini bisa jahilci.

Haka nan kuma shirin zai tabo wasu muhimman lamurra da suke ci wa musulmi tuwo a kwarya, da kuma kirkiro hanyoyi na wayar da kai ta hanyar gabatar da shirye-shiryen da suka dace domin  ilmantarwa.

Kasar Masar dai ita ce kasa ta farko da ta fara kafa radiyon kur’ani tun fiye da shekaru sattin da suka gabata, wanda kuma yake ci gaba da gudanar da ayyukansa.

3684526

 

 

captcha