IQNA

Wata Majami'a Ta Buga Tare Da Raba Kur'anai Ga Musulmi A Masar

16:54 - January 22, 2018
Lambar Labari: 3482323
Bangaren kasa da kasa, wata majami'a ta buga tare da raba kwafin kur'ani mai tsarki a kasar Masar.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya ahbarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na misriyun cewa, majami'ar Marjiigis da ke garin Mina a kasar Masar, ta dauki nauyin bugawa da kuma raba kur'ani mai tsarki ga musulmi na yankin.

Wannan mataki dai ya zo ne da nufin kara karfafa alaka tsakanin msuulmi da kiristoci da kuma yin zaman lafiya da fahimtar juna kamar yadda suka saba tun tsawon shekaru fiye da dubu daya da suke tare.

Wannan lamari ya samu karbuwa da yabo daga malaman addinin muslunci tare da kara karfafa muhimamncin zaman lafiya da fahimtar juna.

A cikin 'yan lokutan baya-bayan na 'yan ta'adda masu dauke da akidar wahabiyanci sun yi ta kaddamar da hare-hare kan majami'oin mabiya addinin kirista  abirane daban-daban  na kasar Masar, kamar yadda kuma suke kai irin wadannan hare-hare na bam a cikin masallatan musulmi wadanda basa bin akidar wahabiyanci.

Amma wani abin ban shawa shi ne, yadda wahabiyawa suka kasa kawo Baraka da tashin hankali tsakanin msuulmin kasar Masar da kiristocin kasar.

3684158

 

captcha