IQNA

Bayar Da Horo Ga Mata Kan Kur'ani A Yemen

22:35 - January 21, 2018
Lambar Labari: 3482320
Bangaren kasa da kasa, ana gudanar da wani shiri na bayar da horo akn kur'ani mai tsarki ga mata a yankin Hadra Maut na kasar Yemen.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na hadramout.net cewa, an fara gudanar da wani shiri na bayar da horo akn kur'ani mai tsarki ga mata a yankin Hadra Maut na kasar Yemen a cikin wannan mako.

Babbar manufar wannan shiri dai ita ce bayar da horo an jysamman ga malaman kur'ani mata da suke koyarwa a makarantu, ko kuma suke da niyyar karantar da kur'ani a makarantu.

Yanzu haka dai shirin na ci gaba da gudana tare da halartar daruruwan mata da suke samun wanann horo mai take ummuhatul muminin a garin Sah na gundumar Hadrmout.

Abin tuni a na dais hi ne yankin Hadmaout yana a gabashin kasar Yemen ne, kuma sun karbi addinin muslunci ne tun lokacin manzon Allah (SAW), kuma yanzu haka akwai mabiya mazhabar ahulul bait (AS) da suke zaunea  yankin.

3683826

 

 

 

 

 

 

 

captcha