IQNA

An Gudanar Da Janazar Babban Makarancin Kur'ani A Lardin Asyut

22:55 - January 20, 2018
Lambar Labari: 3482319
Bangaren kasa da kasa, an gudanar da janazar babban malamin addini kuma makarancin kur'ani sheikh Zahran Farraj a lardin Asyut na Masar.

 

Kamfanin dillancin labaran iqna ya bayar da rahoton cewa, a jiya an gudanar da janazar babban malamin addini kuma makarancin kur'ani sheikh Zahran Farraj a lardin Asyut na Masar tare da halartar dubban mutane.

Dukkanin malamai na birnin sun samu halarta, kamar yadda kuma jama'ar gari daga dukkanin sassa na birni sun halarta, kamar yadda makaranta kur'ani daga wasu sassa na kasar suka halarci janazar shehin malamin.

Wasu daga cikin daliban malamin wadanda shekarunsu sun kai 80, sun bayyana cewa sun samu kyakyawar tarbiya da hoto daga wurin shehin malamin musamman ta fuskar kur'ani mai tsarki.

Wannan babban malami ya kasance makarancin kur'ani mafi shahara  alokacin kuruciyarsa, wanda Allah yaba shi murya mai dadi da salon a musammana  wurin karatun kur'ani mai jan hakula.

An shedi malamin da tsoron Allah da gudun duniya da kuma son jama'a, kamar yadda ya kasance mai son ganin an raya sha'anin kur'ani da son manzon Allah a cikin dukkanin lamurra.

3683454

 

captcha