IQNA

Za A Bi Kadun Saka Sunayen Musulmi Cikin ‘Yan Ta’adda A Amurka Ta Hanyar Shari’a

23:16 - January 18, 2018
Lambar Labari: 3482310
Bangaren kasa da kasa, babbar cibiyar kare hakkokin musulmi a kasar Amurka CAIR ta ce za ta bi kadun matakin saka sunayen wasu musulmi a cikin jerin sunaen ‘yan ta’adda a kasar.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin yada labarai na cibiyar AIR cewa, wannan cbiya ta tabbatar da cewa za ta bi kadun matakin saka sunayen wasu musulmi a cikin jerin sunaen ‘yan ta’adda a kasar ba tare da wani hakki ba.

Bayanin cibiyar ya ce an sanya sunayen wasu daga cikin musulmin kasar cikin jerin sunayen yan ta’adda, alhali ba su da wani laifi bil hasli ma ba a taba kama su da aikata wani laifi komai karancinsa ba.

Cibiyar ta ce ba za ta bari a cutar da mutanen da basu da hakki ba, saboda haka za ta dauki matakai na doka da shari’a domin tunkarar wannan mataki na zalunci da nuna fin karfi da mahukuntan an Amurka suke dauka kan musulmi ‘yan kasa.

Musulmin kasar Amurka tun bayan da Trump yah au kan kujrear shugabancin kasar suka shiga cikin mawuyacin hali, inda ake una musu wariya da cin zarafi a hukumance, kamar yadda kuma basu tsira ba a wajen mutane masu kikayya da musulmi a cikin gari.

3683243

 

 

 

captcha