IQNA

Cibiyar Musulmin Omaha Ta Shirya Zama Da Ya Kunshi Bangarorin Mahukunta

23:31 - October 22, 2017
Lambar Labari: 3482027
Bangaren kasa da kasa, cibiyar msuulmin birnin Omaha na kasar Amurka ta shirya wani zama da ya kunshi alkalai da lauyoyi da kuma jami’an tsaro domin bayyana matsalolinsu.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na 3newsnow cewa, babbar cibiyar msuulmin birnin Omaha na kasar Amurka ta shirya wani zama da ya kunshi alkalai da lauyoyi da kuma jami’an ‘yan sanda na FBI domin bayyana irin matsalolin da suke fuskanta da kuma neman a dauki mataki.

Wannan zma ya mayar da hankali ne kan karuwar kyamar musulmi a kasar da kuma cutar da su da ake yi a wurare, musamman ma mata masu saka lullubi a kansu.

A zaman taron ciyar ta bukaci da a dauki mataki na kare rayukan musulmi da mutuncinsu da dukiyoyinsu daga mutane masu satsauran raayin kyamar msuulmi.

Haka nanuma an ajiye a kan cewa za a gudanar da wani zaman nan gaba kadan tare da wakilan ciyar ta msulmi da kuma hukumar ‘yan sanda ta FPI, inda za a tattauna muhimman batutuwa da suka shafi yadda musulmi za su rika samun kariya.

3655311

captcha